Wa nake so? 182

341 29 4
                                    

*WA NAKE SO?* 💝💝💝
182

WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.com

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*


"Abbah kayi hakuri!"
Ya fada Yana zura hannu a aljihu ya zaro takardar yace

"Na riga na datse igiyar aure na akan ta. Wannan shine hukuncin da zan iya dauka Dan Nan gaba zata iya kisa ma Dan daga wancan har wannan da Allah yayi da karar kwana da shikenan!"

Ido Hajara ta zaro Tayo wajen Aliyu tana kuka. Mikewa yayi ya dire Mata takardar ya bar dakin

Aisha kuwa jikin ta ne duk yai sanyi. Maryama kuwa dadi taji. Mamah ma duk bataji Dadi ba. Momy kuwa murna kamar me.

Kai Abbah ya girgiza yace
"Kiyi hakuri Hajara ki koma gida ki nutsu Zan Masa magana in ya huce insha Allahu Zaki koma dakin ki."

Baba da jikin sa yai sanyi yace
"To Ranka ya Dade Dan Allah a bashi hakuri ya maida tan."

"Insha Allahu."
Nan Abbah ya rufe taron da addu'a kowa ya watse.

Hajara da Baba suka tafi gida. Suna zuwa Baba yai Tai Mata fada Wai ta ja musu yanzu abubuwan da suke samu zasu daina. Domin kuwa a duk  wata sai an siya musu kayan abinci da kudi. Sallah karama Shima ai musu dinki da kayan abinci da kudi. Babba ma ayi musu dinki da layya da kayan abinci da kudi. In an tashi fitar da zakkah har dashi. Gashi ta dalilin ta shi da Mai dakin sa sunje Makkah da Umrah. Ji yayi kamar ya karya Hajara.

Babar ta kuwa Jin abinda Hajara tayi ba karamin tsoro da mamaki ya Bata ba tai tayi Mata fada da nuna kuskure shi kuwa Baba ta abinda suka rasa yake ji.

Haka ya fice bai Kara bin ta kan Hajara ba.

*
Momy na shiga daki ta samu sha'awa tace
"Ke tashi Wai baccin me kike haka ne?"

Mikewa tayi tace
"Wallahi Momy kwana biyu bana Jin Dadi ga kasala nai ta Bacci da na samu Waje."

"Amman Baki fada likita ya duba ki ba?"
"Uhmm!"

"To albishirin ki?"
"Goro."

Tai wata Dariya tace
"Uhmm wallahi an saki Hajara yau!"

"Da gaske?"
Kai Momy ta gyada. Mikewa tayi tana rawa tana fadin
"Wayo sauran daya kenan Amman naji Dadi tana Ina?"

"Sun tafi ita da Baban ta."
"Ikon Allah. Me tayi Amman har haka?"

"Uhmm Ashe Aisha ta daka har cikin jikin ta ya zube."
Ido Hajara ta zaro tace
"Aishan ciki ne da ita?"

"Ya zube ai!"
"Ah kace dole itama na shige Mata domin kuwa ba wanda zai haifawa Aliyu 'da sai ni. Kan itama tayi Waje."

"Ya dai kamata."
"Yanzu ya za ayi to?"

"Ai sai ta tafi kawai Zaki bita gidan nata can zaki samu damar aikata Mata komai."
"Haka za ai Momy na."

Sai ta cigaba da murna an saki Hajara.

*
Suna Shiga daki Aisha ta zuba tagumi. Maryama tace
"Wai ke menene haka?"

"Maryama Amman ai ba Dadi Dan Allah matar sa ce fa Kuma sai ya sake ta akai na ai sai duniya ta zagen."
"Kada ki manta da irin son da Yaya yake Miki Kuma ke kanwar sa ce Dole ba zai zauna a cutar dake ba."

WA NAKE SO?Where stories live. Discover now