Wa nake so? 134

328 40 5
                                    

*WA NAKE SO?* 💝💝💝
134

WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.com

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*



Zaune take a office din nata tana duba wani littafi dake gaban ta bayan tayi round ta dawo. Wayar tace ta dau kara tana dubawa taga sabuwar number. Dauka tayi tayi sallama. Amsawa akai sannan akace
"Doctor An tashi lafiya ya kike ya aiki?"

"Alhamdulillah amman ban gane waye ba?"
"Jannah ce!"

"Oh Jannah ya kike ya gida ina Noor?"
"Gata!"
Ta amshi wayar tace
"Ina kwana ya aiki?"

"Alhamdulillah ya gida da Hajiya?"
"Tana lafiya!"

"To agaishe ta!"
"Zata ji."

"Aha nagode!"
Jannah ta amshi wayar tace
"Doctor ranar friday zan shigo muje radio station tare."

"To shikenan sai kinzo!"
"Yauwah nagode ki gaida Momy."

"Zataji sai anjima!"
Ta fada tana kashe wayar. Ido ta lumshe tana murmushi take ta tuna zuwan su gidan. Kenan su Noor yayan wannan mutumin ne Uncle wa ma taji suna cewa? Ohoo ta manta.

4:00pm
Aka shigo office din ta da sallama. Dagowa tayi tana amsa sallamar Aslam ne ya fara shigowa ya kura mata ido,  kai ta dauke tana kallon system din gaban ta.

Dagowa tayi suka kara hada ido. Kai ta dauke ya saki murmushi ya harde hannu yana kallom ta. Aiki ta cigaba dayi bata yadda ta dago ba.

"Assalamu alaikum!"
Jiddah tayi sallama

"Wa'alaikun salam!"
Suka amsa. Jiddah tace
"Ya ka tsaya anan!"

Fateema ya nuna mata yace
"She didn't welcome me!"
Kallon Fateema tayi. Fateema tayi murnushi tace
"Bismillah!"

Murmushi Jiddah tayi tace
"Thank you!"
Ta kama hannun sa suka karasa ciki. Zama tayi shima ya zauna.

"Ina yini Doctor?"
"Lafiya Alhamdulillah ya gida?"

"Alhamdulillah!"
Ta mika mata files din hannun ta tace
"Na shiga na amso result din ne."

Amsa Fateema tayi ta zare envelope din sannan ta bude tana karata abinda ke a ciki. Idon ta akan takardar tana dubawa wanda Aslam ya tattara gaba daya hankalin sa ya maida kan fuskar ta yana kallon ta yana sakin murmushi. Itama Jiddah kallon ta take. Can ta dago tana kallon Aslam da ya kurawa Fateema ido. Zungurin sa tayi da hannu ya juyo a hankali ya kalle ta ya dage mata gira alamar
"Ya dai!"

Murmushi tayi tace
"Matar aure ce dai!"
"Waya fada miki?"

Fuska ta bata tace
"What did you mean to?"
Murmushi yayi yace
"Antyn kishi!"

Murmushi tayi tace
"Kar nayi kishin abinda nake so ne?"
"No kiyi!"

Tai murmushi. Fateema ta ajiye na Aslam ta dauki dayan na jiddah ta duba shima sannan ta ajiye tace
"To from dis result it shows that both of you are fine. Zaku iya haihuwa lokaci ne kawai bai zo ba."

Ajiyar zuciya suka sauke. Fateema tace
"Sai dai kila matsalar wata kila daga baya ne abinda kika yi ne! Kisan planning yana da matsala wani lokacin allura tana sa jinkiri akan daukar samun ciki. Yanzu dai abinda zan ce baki da matsala tinda aladar ki ta saitu to ba matsala domin allura na bada matsala wani ta dauke miki zubar jini wani ta birkita miki wanda kila daga nan a samu matsala dan haka muke cewa aje cibiyar kiwon lafiya dan auna jinin ki aga wane tsari za'a a saka ki. Matsalar kuma ke kinga baki shiga dakin ki ba ace baki tabbatar ma kiina haihuwar ba amman kinje kin fara planning dan haka yana dakya ana wayar da kai akan wannan matsalar in har planning kake so kaje cibiyoyin kiwon lafiya dan a gane wanne ya dace. Yanzu ba abinda zance sai dai nace Allah ya kawo zuri'a mai albarka ya kawo haihuwa nan kusa Amin. Fatan alheri gareku!"

WA NAKE SO?Where stories live. Discover now