Wa nake so? 146

345 34 6
                                    

*WA NAKE SO?* 💝💝💝
146

WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.com

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*

Zaune yake falo yana aiki a system din sa. Jidda ce ta shigo cikin kwalliya mai kyau ta zauna a gefen sa tace
"Honey wata fa yayi banji alert a."

"Haka ne wai so nake kiyi lissafi da kayan fadar kishiya ai."
"What?"

"Eh ko irin nata kike so?"
"Me fa?"

"Laifen!"
" honey auren ya taho ne?"

Kai ya dafe yace
"Am sorry dear an saka lokaci remains two month insha Allahu."

Wani abu ta hadiye da kyar tace
"To amman ni dai ka turon nawa kawai ina bukatar kudin ne nan kusa akwai abinda zanyi."

"An gama uwar gida ran gida."
Ya mika mata wayar sa yace
"Kiyi transper duk yada kike so."

Amsa tayi ta saki murmushin da yafi kuka ciwo tace
"Nagode!"

Turawa tayi ta bashi. Ya ajiye yace
"To me kike ganin za ayi a bikim?"

"Zanyi tinani kan time dim."
"Yauwaj."

"Baka fada min wacece amaryar ba!"
murmushi yayi yace
"Ki kwantar da hankalin ki zaki ganta as suprise!"

"Ni dai bana so kawai ka fadamin."
"To in baki santa bafa."

"Ina son na santa tinkan bikin ne?"
"Zan fada miki but not now!"

"Promise!"
"I promise you!"

"Thanks!"
Ta fa tana mikewa tayi cikim daki.

Tana shiga ta daura hannu a ka kamar zaya kurma ihu sai ta zauna ta dauki wayar ta. Tana kuran Najah ta dauka tace
"Najah wai me kuke yine? Bikin saura wata biyu fa."

Tsaki tayi tace
"Ki kwantar da hankalin ki zan shigo zuwa jibi bana gari."

"Yanzu Najah har jibi nifa shiyasa Khady tafi min abinda nake so da ita ce zuwa zatayi a gobe goben nan duk inda take."
Dariya Najah tayi tace
"Shikenan in nazo kyaji dalilin cewa sai jibin sai anjima."

Khady ta kira tana dauka tace
"Ya dai?"

"Kema kin sani ai."
"Meya faru?"

"Auren Aslam ya kusa fa."
"Haba dai?"

"Wallahi saura waya biyu."
"Ikon Allah akwai wani malami zanje wajen sa amman ki kara samo mana information akan yarinyar nan."

"Yaki fa ko yanzu yaki fadan amman dai munyi magana yanzu yace zai fadan kan time din."
"Gud! Ki kwantar da hankalin ki dan Allah."

"Insha Allah."

*
Kwana biyu gaba daya ta daina fita duk ta shiga damuwa ta rame ta fita a haiyacin ta. ko wayar bata san ina ta shiga ba. Momy tayi fadan, tayi nasiha, tayi lallashin amman duk a banza dan haka itama ta share ta kawai.

Ta auri zaman daki sai kallon picture din Fu'ad ko karatun alkur'ani. Duk dai ta fitar da rai da rayuwa da jin dadi.

shi kan sa Aslam da yaje asibiti akace bata nan yai mamaki ya kira wayar ta yafi sau nawa amman bata dauka. Yau ma yana dawowa daga aiki ya wuce wajen Fateema amman bata nan wannan yaza ya nufi gidan nasu kawai. Yana zuwa yai parking.

WA NAKE SO?Where stories live. Discover now