Wa nake so? 171

442 33 2
                                    

*WA NAKE SO?* 💝💝💝
171

WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.com

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*

Zaune suke iyayen akan kujera yaran kuma gaba dayan su a kasa. Yaa Abubakar ne zaune sai Yaa Usman da Umar da Farouk sai Aliyu da Yaa Muhammad dake zaune a gefen su. Sai Yaa Mustapha,  Umar,  shu'aibu,  da İbrahim suma

Dayan gefen kuma Aisha ce zaune ta takure waje daya cikin lifayar da aka saka mata Maryama ce a gefen ta sai Anty Khadija a daya gefen nata sai Anty Hauwa da Fatima da Nusaiba.

Momy da Mamah da Mama da Umma akan kujera sai Abbah da Mr president da Baba suma akan kujera. dakin tai tsit kamar ruwa ya cinye su. Gyaran murya Abbah yayi yai addu'a sannan yace
"Alhamdulillah kamar yadda akai taro aka gama lafiya muna fatan Allah ya basu zaman lafiya ya kade fitina."

Duk dakin suka hada baki suka amsa da Amim. Abbah yai gyaran murya yace
"Ba komai yasa na tara ku anan ba sai dan na hada ku da yar uwar ku. Ba ina nufi dan ta auri Aliyu ne kawai ta zama yar uwar ku ba a'ah yar uwa ce ta jini gareku domin kuwa 'ya ce ga Hafsa kanwar Mamah ku ina fatan kun gane?"

Yaa Abubakar da Yaa Usman sun san komai akan Mama da yadda akai auren har mijin ya mutu ta koma gida ta kara wani auren. Amman Yaa Aliyu da Umar da farouk basu san komai ba kamar yadda itama Aisha kanta ya kulle.

Nan Abbah yayi bayani filla filla. Kan Aisha na kasa ba abinda  take sai kuka. Mama ta mike ta dawo kusa da ita ta rumgume ta. Aisha ta rumgume mama tana sakin wani kukan mai taba zuciya duk wanda yake dakin sai da ya tausaya musu Aliyu kuwa kukan Aisha yake ji har cikin zuciyar sa.

"Ki yafemin Aisha ki yafe dan Al..."
Da sauri Aisha ta daura hannun ta a kan bakin mahaifiyar tata tana fafin
"Baki min komai ba Mama kawai dai ina kewar kine a matsayin uwa ta. Amman Umma ta min duk abinda wata uwa ya dace tai wa yar ta. Ki godewa Yaa Muhammad a kullum shike kara tunasar dani ke da soyayyar ki ta dalilin sa ne yasa kullum kike cikin zuciya ta ban taba mantawa dake bakullum ina saka ki a addu'a ta Amman Mama me yasa kika tafi baki kara juyowa gareni ba? Bayan ni kullum buri na da fata na nazo naga Mama ta."

"Ba laifi na bane. Kamar yadda nasan kin samu labari akan cewa ba mahaifi na ne ya aura min aure ba kanin sa ne ya dauran aure saboda Mahaifina bai so wannan yasa muka bar garin kuma ko bayan aure Bana zuwa gida dan da na taba zuwa sai da nayi danasanin zuwa. Haka na zauna da mahaifin ki ba abinda zan ce da mahaifin ki da dangin sa dan sun rike ni da amana. A haka Har Allah ya amshi mahaifin ki da banyi niyyar tafiya ba amman abinda Mahaifin ki ya fadamin yasa na ce zan tafi dan kan ya rasu ya roken in ya mutuna koma gida na bawa Mahaifina hakuri haka akai da nazo tafiya dake ne Baban ki yace ba zan tafi dake ba wannan shine yasana tafi bayan na koma gida dakyar mahaifina ya amshe ni da sharadin zai aurar dani ga wanda yaso kuma ba zan koma garin da kike ba. Haka na yadda a satin aka dauran aure wanda muka bar kasar gaba daya. Kuma a lokacin mahiafin yace in na wai waye ki a rayuwa bai yafe min ba. Ban kara dawowa nigeria ba sai bayan shekara goma domin Abbi mahaifina ya hana sam na zo gida kuma da nazo sai da ya karai min gargadin kada na soma zuwa garin nan. Bayan mun koma sai da nayi shekaru na kara zuwa wanda wannan shine zuwana na uku bayan tafiya ta. Kinji yadda abin ya faru  nasan ni da yan uwa na muna da laifi na rashin bi halin da kike tinda ko bamu zo ba ai zamu iya sanin a halin da kike amman bamu bi ba ki yafe mana Aisha dan Allah ki yafe mana. Kina raina da tunani na ba ranar da zata fito ban tina dake da mahaifin ki nai musu addu'a ba. Ba abinda nake kauna a duniya sama dake Aisha. Ki yafe min Aisha ki yafewa mahaifi na da yan uwa na."

WA NAKE SO?Where stories live. Discover now