END OF BOOK 1
Aneesa farkawa tayi kawai ta ganta kan cinyar Khairee na goga mata hankicif din dake jike a hanun ta, zumbur ta mik'e tabisu da kallo d'aya bayan d'aya harsai data sauke ,idon ta kan Matar da takira da Malama wanda ita ma itan take ,kallo ,lokaci guda idanun ta suka ciko da kwala 'a hankali ta bud'e baki tace.
"Malama karki cemun Walida itace yar baiwa karki ceman walida ita ce abun dana barmiki tun kafun ta zama ,mutum ?".
Malama dake girgiza kai ,itama tana hawayen tace .
"Aneesa koban fad'a miki ba kamanin ku ze gaya miki ,ita ce wacce kika tsalake ,kika tafi kika barta cikin wahala , Aneesa dube ki dubi yanda kika ,koma 'amman ko tunanin yarki bakiyi bare kisan a irin halin da take ciki a rayuwan ta 'Aneesa 'anya kuwa hakkin ta ze barki ?".
Aneesa kuka take shek'a ,kamar zata shid'e tace.
"Malama tun randa na tsalake Walida nabar ta zuciya ta, ta kasa ,samun ,nutsuwa duniya ta ,tasauya min ban samu kwanciyar hankali ba harsai dana koma 'adamawa don ,naje na d'auko ta musha wuyar da zamushi tare da ita 'amman kash sai banyi sa'a ba ,don a lokacin danaje rugan ku sai ake ceman ai kunyi gobara kuma duk yan rugar sun rasu babu wanda ya fito darai , a wannan ranar da naji wannan *BAK'AR RANA* nayi kuka harna gode Allah kuma duk randa na tuna 'abun yana tab'ani fiye da tunanin ki, kuma ina son ki yarda ,dani bawai nabar Walida bane don bana k'aunar ta ko don abun da, dangin ta suka man ,nabar tane saboda bani da zab'i bakuma naso tasha wuya arayuwan ta 'ashe wuyan ,nata yana gaba" kawai ta kuma fashewa da kuka.
Kowa tausayin ta ya farayi a guri sudai su Khairee basuyi mamakin jin Aneesa nada yar ba saboda ,dama ta sanar dasu abun daya basu mamaki shine jin Walida itace d'iyar Aneesa duk shid'in ma ba 'abun mamaki bane tunda ga kamaninsu ya nuna .
Malama tashi tayi ta shiga d'akin ta ,ta d'auko wani akwatin k'arfe ta bud'e ta fiddo wani takar da 'dayake nad'e ta fito , mik'awa Aneesa tayi, cikin rashin fahimta da tunanin takardan miye kuma wannan ta k'arb'a tarik'e tana kallon Malama 'alamun kiyi min bayani .
"Nasan zakiyi mamakin wannan takardan kota mecece , Salihijo ne yace abaki ,kafun Allah yayi masa rasuwa".
Aneesa saida k'irjin ta yayi wata mummunar fad'uwa dajin cewa Salihijo ya rasu bata san lokacin da tace.
"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un yarusu fa kika ce Malama ?".
"Kwaraikuwa Salihijo ya rigamu gidan gsky bayan kin gudu kin barmu da wata shida Salihijo yazo har rugar mu neman ki lokacin bayan yayi nadama sannan ya gane gsky Amman yayi rashin sa'a be sameki ba , be karaya ba ya bada lambar wayan sa kan duk randa 'Allah yasa kika dawo mukira mu sanar masa ,Salihijo yakai wata biyu yana jelen zuwa ko Allah zesa kin dawo amman shiru cikin ikon ubangiji ranar da 'Allah ze d'auki ran Salihijo bayan yayi salama dayan rugar su kan ze tafi legos fatauci be tsaya ko ina ba sai rugar mu shine ya bani wannan takardan akan idan kin rugashi dawowa nabaki ya kama hanya ,ya tafi a wannan rana da magariba mukaji labarin rasuwan Salihijo saka makon had'arin motar da suka samu tow kinji dalilin dayasa na 'ajje wannan takarda kan ko shekara dubu zeyi duk randa kika dawo zancika masa 'alk'awari duk da babu wanda ya tab'a bud'e ko takardan bere yasan miye aciki , bayan rasuwan Salihijo munshiga cikin wani mawuyacin talauci wanda ko abinci da zamuci gagaran mu yake gashi duk shanun da muka malaka sunyi wani 'irin cutar dayayi sanadin mutuwan su dama Salihijo shike kula da suturan Walida ',abincin ta daduk wani abu na buk'atar ta naso na bawa ,Walida ilimi koda na firamare ne tow Amman bani da k'arfi a kullum na kalli Walida ,duk da banice na haife taba nakan tausaya wa rayuwan ta idan aka ce miki lokacin sanyi ,yayi ko damuna tow muna cikin mawuyacin hali saboda lokacin ,ne ciwan Walida ke tashi gashi bamu da halin zuwa 'asibiti bamu tab'a tunanin walida zata rayu takai yanzu ba duk da 'ayanzun ma 'Allah be fitar da ita daga cikin wuyan ba tow danaga rayuwan k'auyen baze kaimu ba yasa na tattaro Walida tare da bawa mak'ocina labarin idan kindawo ya sanar dake munkoma bauchi gurin k'anwa ta da zama tare kuma da k'arb'an nambar wayan shi kan zamu dinga kiran shi lokaci lokaci , bayan komowar mu bauchi da wata uku mukaji labarin iftila'in daya faru a rugar tamu ,muna rayuwa cikin rufin asiri shine Walida ta fara ciwo kamar wasa ya zama babba wanda muka d'auko ta zuwa asibitin bakas ,shine suka turamu kano, wannan shine labarin abun daya faru a tak'aice".

YOU ARE READING
BAK'AR_RANA
Short StoryMiye ban bancin ki da karuwa? Zina kuma kinyi shi don Haka kije Allah ya tsine miki!!! Innalilahi wa inna ilaihi ranjiu'n Abba karkamin haka karka k'arasa kassara min rayuwa Abba Anya kuwa kai ne mahaifina ? Karki damu Aneesa ni zan zame miki komai...