Ayi mun afuwa na danyi mistake Wannan shine babi na biyu
Cikin Sauri ma'aikatan asibiti suka karb'e shi ba'a wani b'ata lokaci ba suka shigar dashi wani d'aki, Anty Faty dake faman kuka tana sambatu kamar wata zarariya.
"Shike nan wannan mayyar yarinyar ta gama mana da mahaifiya sannan kuma yanzu tana son kashe min d'a wlh Zaid ya mutu ta dalilin ta duk inda ta shiga a fad'in k'asar nan sai na sa 'an kamo ta an d'aure ta , "..
Anty Safina dake ,kusa da ita ce keta bata hakuri amman Anty Faty idon ta ya rufe masifa kawai take surfawa, Nadiya da Akram dasu Badiya sai kuka suke...
Bayan Awa guda ,da shiga dashi cikin d'akin doctor ya fito , da sauri Anty Faty ta nufeshi tana "likita ya jikin nashu ina fatan babu wani matsala ".
D'aga mata kai yayi kawai yana cire safar hanun shi yace "ku sameni a office yanzu"..
Ita da Anty Samina suka shiga , duk sunyi jigum jigum suna sauraren abunda , Doctor Salman ke fad'a..
"ku binciki Zaid akwai abunda yake so yana cikin matsala zuciyar shi yana daf da shiga wani hali matsawar be samu abunda yake so ba.
don a halin da 'ake ciki yanzu jinin shi ya hau sosai, amman karku damu insha Allah komai zaiyi nomal"..
"Tsananin tashin hankali Anty Faty ta shiga , kukan ma kasa zuwa mata yayi jiki babu kwari ta mike ta fice Anty Luba na biye da ita
*********
Babban asibitin gombe ya cika mak'il da Jama'a kowa sai kai komo yake.
Kofar get d'in asisibitin ta tsurawa ido wanda ze sadata da waje mamaki kawai takeyi na ganin cenzawan asibitin lokaci goda komai ancenja masa fasali zuwa na zamani , sai tana ganin abun kamar amafarki sama da shekara goma shabiyar tana cikin asibitin bata tab'a fitowa ba sai yau, wasu zafafan hawaye ne suka fara zirya akuma tun ta lokacin data saka hanun ta, tabude kofar asibitin tafita, tafiya kawai take ba tare da tasan inda zataje ba, Farace amman ba cen ba tana sanye cikin wani hijabi ruwan ganye duk ya kod'e sai da tayi tafiya me balain nisa ,sannan ta tsaya jikin wani Restaurant tana hutawa..
"Bilki duk randa na tuna cewa ,watan wata rana zamu rabu nakan shiga tashin hankali , da mutuwa tana salama kafun ta d'auki mutum da zance da ita ,ta fara d'auka na kafun ke saboda gsky ina ganin idan kin rugani mutuwa bazan iya rayuwa babu ke ba" murmushi tayi tana shafa cikin ta daya girma yakai watan haihuwa tace"Malam kenan tow kana tunanin ,ni kuma idan babu kai zan iya jin dad'in rayuwa tane , karfa ka manta kaine gatana bani da kowa yanzu sai kai , insha Allahu ma ,muna tare dakai kai dai yanzu kayi fatan Allah ya sauke ni lfy "...
Shafa cikin ta yayi ,yace "Allah ya sauke ,ki lfy Bilkisu na zan so naga jinina araye kafun Allah ya d'auki raina Ubangiji ya sa wannan shine me zama "....
Wasu zafafan hawaye ta goge bayan ta dawo daga dogon tunanin data fad'a ,tana "Allah ya jik'an ka Malam , bani da gata 'ayanzu bani da inda zani , hak'ika anzalun ceni Amman akwai Allah.
Cikin Restaurant d'in ta shige ,zaune taga wata yar buduruwa tana zaune tana yankan Albasa da salama ta k'arasa gareta..
"Ya Rinya ina wuni ".
Buduruwar dake yankan Albasan ta d'ago da kanta , ganin matar dake gaishe ta ba yarinya bace yasa tace.
"Ina wuni Baba lfy kow abinci kika zo saya ?" Gyed'a mata kai tayi tace "A'a don Allah me wannan wajen ,nake nema ko zaki d'an iya min magana da ita " babu musu yar budurwan ta mike taje ta kira mata ogarsu, dake ogar tasu bata d'auki duniya da zafi ba kuma tana da kirki babu musu ta mik'e taje..
"Bismillah Baiwar Allah ga wuri ki zauna" ba musu Bilki ta ja kujera ta zauna " Allah dai yasa lfy kike nemana baiwar Allah " lfy qlau ni sunana Bikisu niba yar garinan bace zuwa nayi ,yau kwanan d'aya da zuwa(ta fad'a mata hakane saboda bata son tasan sirrin ta) don Allah idan babu damuwa ina son ki bani aiki a gurinnan ,naki ,ko kuma ki nema min gidan aiki"..

YOU ARE READING
BAK'AR_RANA
Short StoryMiye ban bancin ki da karuwa? Zina kuma kinyi shi don Haka kije Allah ya tsine miki!!! Innalilahi wa inna ilaihi ranjiu'n Abba karkamin haka karka k'arasa kassara min rayuwa Abba Anya kuwa kai ne mahaifina ? Karki damu Aneesa ni zan zame miki komai...