page 2

4.6K 167 5
                                    

*MR MA'ARUF...*

® '''Written'''
_By_
*_Seemaluv👄_*

© *GORGEOUS WRITERS ASSOCIATION*

https://www.facebook.com/groups/1649808818646464/

                               Page 2

Nan Na'eema ta d'aga kai ta kalli agogon da ke jikin bango.
    "Ammi? 6:30pm fa yanzu, Naga har yanzu Bro Ma'aruf basu shigo ba."
Na'eema ta fadi haka gamida tashi zaune.
Ammi yunk'urawa tayi ta tashi tare da cewa.
    "Eh to kila aikin su ne ya tsaida su."
Abinda Ammi ta fad'a kenan ta wuce part d'in ta, Sannan itama Na'eema ta tashi ta wuce d'akin su.
  Suhaila da Na'eema sun gama secondary school d'in su, Yanzu jira suke kawai result ya fito sannan su sami damar wucewa makarantar jami'a.
  *Around 7:00pm* Mr Ma'aruf ya dawo gida bayan yayi parking motar shine ya fito ya shiga cikin gida a gajiye.
   Koda ya isa harabar parlor mai aiki ce ya iske tana ma'ana maman talatu tana ta kai da komawarta, Ganin shine yasa ta tsaya suka gaisa tayi mashi sannu sannan Mr Ma'aruf ya zarce d'akin shi.
Bayan shigar shi d'aki ne ya aje jakarshi sannan ya cire suit d'in jikinsa, Mr Ma'aruf towel ya d'aura a jikin sa tukunna ya shige bathroom da alama wanka zaiyi.
  Bayan 'yan mintoci k'alilan ya fito ya goge jikinsa da k'aramin towel daga bisani ya ciro k'ananan kaya white polo T-shirt da wando ya sanya sannan ya d'auki wayar shi ya bar d'akin zuwa parlor.
  Mr Ma'aruf koda ya shigo parlor iske Ammi yayi zaune tana kallon TV news Suhaila kuma tana danna wayarta as usual.
  Mr Ma'aruf k'arasawa yayi gaban Ammi ya zuk'unna har k'asa ya gaishe ta ta amsa a karkace, Sannan Mr Ma'aruf ya koma zauna a three seater.
    "Wai shin ina Haidar ne? Shi bazai dawo gida bane?."
  Ammi tayi maganar cikin zafin rai.
    "Haidar kam I don't think zai dawo yanzu don aiki ne sosai agaban shi yanzu."
Cewar Mr Ma'aruf.
    "Wane irin aiki ne dabazai dawo gida ba ya huta kamar kowa ba? Iye Ma'aruf? Nasha gaya maka ka daina bama Haidar aiki mai wahala a office saikace ba d'an uwanka ba?."
Nan Ammi ta cigaba da fad'a ta inda take shiga ba tana nan take fita ba yadda kasan  dama ajirace take dashi.
  Suhaila ce ta shiga maganar da cewa.
    "Haba Ammi kiyi hak'uri mana wata kila ba laifin bro Ma'aruf bane..."
Suhaila bata kaiga rufe baki ba Mr Ma'aruf ya daka mata tsawa da cewa.
    "Suhaila! Baki da kunya ko? Tashi ki bar wajen nan kafin in b'ab'b'alla ki."
Cikin b'acin rai Suhaila ta tashi cike da takaice ta wuce d'akin su, Bayan wucewar ta ne Mr Ma'aruf ya mik'e tsaye gamida sanya hannunsa d'aya cikin aljihu yace.
    "Ammi, Haidar d'an uwana ne bazan so wani abin cutarwa ya cutar dashi ba kuma dole ya tsaya company yayi min aiki whether you like it or not domin kuwa a k'ark'ashi na yake kuma company d'in nan duk k'aruwar mu ne baki d'aya."
  Mr Ma'aruf na gama fad'in haka ya juya ya wuce d'akin shi, Nan Ammi ta saki baki cike da mamaki da d'aurewar kai tana kallonsa har ya b'ille sannan tace.
    "Lallaima Ma'aruf... Har kayi girman da zakana gayamin magana? To dole na d'auki mummunan mataki a kan ka tun kafin abun yayi nisa."
Abinda Ammi ta fad'a kenan tayi k'wafa ta maida kallon ta ga TV.







#TeamMa'aruf

*SEEMALUV HAUSA NOVELS."
 

 

MR MA'ARUFWhere stories live. Discover now