*MR MA'ARUF...*
® '''Written'''
_By_
*_Seemaluv👄_*© *GORGEOUS WRITERS ASSOCIATION*
https://www.facebook.com/groups/1649808818646464/
Bismillahir Rahmanir Rahim...
Gabatarwa a tak'aice...
Mr Ma'aruf, Haidar, Suhaila, Na'eema, 'Ya'ya ne ga Alhaji Ango Abdullahi
Alhaji Ango Abdullahi asalin d'an garin bauchi ne, Hajiya Fatima da Hajiya Hannatu matansa ne na sunnah kafin Allah yayi masa cikawa.
Mr Ma'aruf da Suhaila 'ya'ya ne ga hajiya Fatima, Haidar da Na'eema 'ya'ya ne ga Hajiya Hannatu
Mr Ma'aruf shekarun sa 35, Shi kuma Haidar shekarun sa 29, Suhaila Da Na'eema 'yan watanni ne tsakanin su 18.
Hajiya Fatima tare da kishiyar ta Hajiya Hannatu sun zauna zama na kishi tare da kyautatawa juna a garin bauchi.
Hajiya Fatima ta rasu ne Suhaila nada sati biyu da haihuwa bayan mutuwar Alhaji Ango Abdullahi da wata d'aya ya kuma bar Hajiya Hannu da cikin wata 7.
Haka Hajiya Hannatu ta rik'e komai na gidan yazamana saj yadda tayi da komai.*** *** *** *** *** *** ***
Na'eema ce ta shigo parlor a guje tana dariya rik'e da waya a hannun ta Suhaila na binta da gudu.
"Na'eema wai meye haka? Ki bani phone d'ina mana!."
Shigowar Ammi cikin parlor d'in ne yasa Na'eema komawa bayan Ammi ta b'oye.
"Ha'a wai k'alau kuke kuwa? Zaku fara abinda kuka saba ko? Don kunga Haidar baya gida."
Ammi ta fad'i haka tana k'ok'arin raba jikin ta da Na'eema.
Hakana yasa Suhaila ta sami dama ta fizge wayar ta tare da cewa.
"Zaki gane kin tab'amin phone Na'eema, Zaki zo ki same ni."
Na'eema gwalo tayiwa Suhaila hakan yasa Suhaila karkad'a kai alaman zaki gamu dani, Sannan Suhaila ta juya ta wuce.
Nan Ammi ta sami waje ta zauna Na'eema ta bita ta kwanta saman cinyar ta tamkar wata k'aramar yarinya cike da nuna shagwab'a.
"Wai don Allah ke kam yaushe zaki girma ne Na'eema? Ke ko kunyar kwanciya bisa jikina ba kiyi!."
Na'eema dariya tayi gamida yin ajiyar zuciya tace.
"Haba Ammi, To duk duniyan nan in ban rab'e ki ba wa zan rab'a? Ke kad'aice nake da ita duk fad'in duniyar nan fa."
Ammi ya tsine baki tayi gamida cewa.
"Ke kika sani dai."Kuyi hakuri wannan page d'in bashi da yawa, Somin tab'i kenan.
*SEEMALUV HAUSA NOVELS GROUP*

YOU ARE READING
MR MA'ARUF
Romance"Innalillahi Wa inna ilaihi raji'un... Ummi? Ummi don Allah ki tashi, Ya salaam! Yaya Haidar ku zo don Allah Ummi tana convulsion..."