REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS💭💭💭
we don't just entertain and educate,But we also touch d heart of the reader's
MIEMIEBEE👄 A WANKI GARORI
🌹By Sad-Nas🌹
Dan Allah ina neman wannan book d'in daga farkon shi zuwa page 54 domin in had'ashi in document,wanda yake dashi ya taimaka ya tura zuwa grps ko dai ku turo min please👏🏻
LAST PAGE60
Boka ya kalli Yamal yace "Ke! Kinga dena bina,danni kaina bansan inda na nufaba,sannan a wannan zamanin da muke ciki mutane sun dena taimako babu wanda zai karb'eni barema idan aka ganni yare dake,dan haka ki koma gida kawai"
"Haba Boka taya zaka ce min haka,basai ka tsafesuba su bamu masauk'i da dukkan abinda zamu buk'a tunda aikinkane?"
Dariyan migunta Boka yayi yace "Gaskiyar Hausawa da suke cewa Yaro-yaro ne,to ke inbanda dak'ik'anci irin naki idan kura tana maganin zawo tayiwa kanta mana,nadai yi nasarar taro kud'ad'e da yawa tagun mutane irinki irinki,dan haka k'arya kawai na miki kuma aiki dana miki a baya kikaga ya yuwuma gun wani k'asurgumi naje na biyashi ya had'amin maganin da kikawa k'anin mijinki da matarsa har kikaga yayi aiki,dan dama abin dace ne."
Yamal ta tsaya tana sauraron Boka yaci gaba da cewa "Nima koya nayi na k'arya,kuma ta hakanne na lalata matan aure da dama marasa wayo da tawakkali irin naki saboda nasan bani da amfani tunda na samu cutar k'anjamau ta hakanne na rabawa duk matan da suke kawo kansu guna da sunan inyi musu aiki,kema kuma nasan kina dashi yanzu haka,dan haka ki kama gabanki nima zanje wani gurinne in samu in cinye wannan dukiya na jama'a dana tara tagun sayawa kaina abubuwan dadi inyita ci kafin lokacina yayi."
Boka yana gama fad'in haka ya k'ara gaba,baiyi nisa ba yaga wasu mutane marasa kyan gani,da ganinsu kasan ba mutanen arziki bane suka capkoshi suka had'asu gu d'aya shida Yamal suna cewa "Meya kawoku cikin jejin nan" nan take Yamal ta rud'e tace mijinane zamu shiga gari ne" Boka yace "Wlh karya takeyi ban santa ba ina dai k'ok'arin shiga garine"
Nan dai d'aya daga cikinsu yace "Tunda kace ba matarka bace barima ka gani" nan ya fisgo Yamal ya fara cire mata kayan jikinta yace "Me kake rik'e dashi a hannun ka?"
Boka cikin razana yace "Kullin kayanane kawai" Yamal daketa basu hak'uri tace "Wlh k'aryane kid'inane a ciki zai gudu min dashi ku duba ma ku gani" nan suka karb'e kayan suna zazzageta sukaga kud'ad'ene masu yawan gaske,nan sukasa dariya sukacewa Boka "K'arya zaka manan?" Nan suka shiga zaneshi suna kai masa duka yayi laushi sosai sannan suka ce dashi "Maza kabar nan kafin mu tsayar maka da numfashi" Boka najin haka ya d'iba a guje jiki duk tsamin duka da yasha. Ita kuwa Yamal ganin abinda suke shirin aikata mata yasa ta gama tsorata tanacewa "Dan Allah karku cutar dani wlh inama d'auje da cutar k'anjamau" suka sake sa dariya sukace "Ahaf ai mud'in duk jirgi d'ayane ya kwasomu ba wani sabon abu bane ai" Haka suka mata ba dad'i gaba d'ayansu gasu k'attai su biyar,suna ganin numfashin ya fara baya-baya suka kwashi kud'ad'en gaba d'aya sukayi saurin barin gurin.
Yamal ko kukanma bata iyayi saboda suma datayi agun.Ayau aka kawo Hanifa Amarya d'akin Angonta Yazid. Murna agunsu baya misaltuwa,bayan d'an nasihu da aka musu ne Daddy yace duk su wuce d'akunan su,garin mik'ewa da zasune Nabila ta kasa tashi sakamakon maranta daya rik'eta. Su Hajiya Nana suna ganin haka suka san cewa Haihuwane dan dama ta shiga watan haihuwan ta,kan ayi hanzarin d'agata tuni paya ya fashe cikin gaggawa suka wuce da ita d'aki wanda a lokacin har kan d'a ya fito,ganin haka yasa suka kimtsa mata shinfid'i suna mata sannu da taimakon Allah sai ta haifo d'iyarta Mace santaleliya. Murna sosai wannan gida ya kasance bayan d'an kimtsa mata jiki da sukane aka wuce da ita asibiti domin a duba lafiyar ta,dayake babu wata matsala da aka ganine yasa aka sallamosu suka dawo gida.
Nan dai Yazid yake cewa Hanifa "Lallai kin shigo gidannan da alkhairi" murmushi tayi ta kwanta a jikin sa tana b'oye fuskar ta.
Al'amarin Yamal kuwa wasu matane sun fito gona nan suka ganta kwance babu komai a jikinta,kuma da alamunma bata ko motsi,sun tsorata sosai dan haka suka wuce sunata zance sai suka had'u da wasu police nan suka gaya musu abinda suka gani.
Babu b'ata lokaci suka kai su gurin,take suka nemi abu suka rufe mata jiki aka d'auketa zuwa wani k'aramin asibiti,koda suka isa sai likita ya tabbatar musu da cewa ai ta rasu. Allahu akbar,Yamal dai ta tafi batare data tuba ko neman gafaran wanda ta cutar dasu ba.
Kafin a sake suturceta ne aka d'auki hotonta anata sanarwa a gidan TV da radio akan ana cikiyar Iyayenta domin suzo su d'auki gawarta.
Koda Iyayenta suka sami wannan labari sunyi bak'in ciki matuk'a,musamman ma labarin da suka sake samu daga bakin police.Gidan Alhaji Abbakar duk sunga hotonta a gidan TV nan take Miemie tace "Yamal na yafe miki har abada" ta kuma gayawa Ammar komai tare da nemawa Yamal yafiya agurinshi,Ammar ya girgiza sosai amma duk da haka ya yafe mata,sai kuma tsakaninta da mahaliccin ta.
_😔Hmmmm Allah kasa mufi k'arfin zuciyanmu,Allah karka bamu ikon sab'a maka kota wace hanya,Allah ka bamu ikon yin abinda zai kaimu ga samun rahamar ka ameen._
Shi kuwa Boka tun daga lokacin daya rasa kud'insa ciwo mai tsanani ya makashi wanda hakan shine ajalinsa shima.
Yau ake sunan 'yar Nabila da Nabil,inda yarinyar taci sunan Mummy amma ana kirantane da (Afrah) Su Meela ma ciki ya girma sai cin alale take a gidan suna ana tsokanarta ita da bilki dan duk sunyi nauyi.
Laila kuwa ta shiryu ta tuba ta maida al'amuranta ga Allah. Fatima ma murna take dan ta samu juna biyu sati biyu da suka wuce,nan Miemie taketa tsokanarta agidan sunan tana cewa "Tunda ke naki bak'on baya son Alale kodai D'an wake zan dafa miki ne?"
Suka sa dariya inda Jiddah ta fito da katin aurenta daga cikin jakarta ta mik'awa Miemie akan ta rabawa mutanen gidan. Nan aka sa gud'a ana tayata murna inda Miemie takaiwa su Mummy nasu sannan tazo tanata rabo,nata daya rage guda d'aya saita Mik'awa Ammar dake zaune akan kujera sudeis yana ciyar shi tace "Ina gayyatar ka zuwa auren k'awata,da fatan duk wasu shagulgula za'ayi damu kuma da fatan tun bikin saura sati d'aya Miemie zata tafi gida dan itace babbar k'awa?" Ajiye Sudeis yayi a gefe ya mik'e tsaye tare da janyo hannunta zuwa d'aki duk 'yan parlour'n suka sa dariya suna binsu da kallo.
Rungume shi tayi tace "Allah ya barmu tare My Cream mutu karaba takalmin kaza"
"Ameeeen My Bride" ya fad'a yana kai mata tsunba,nan saiga Sudeis ya shigo yana ganinsu haka yace "Nifa to?" Murmushi sukayi Miemie ta janyo shi garesu duk Ammar ya rungumesu suna masu jin farin ciki har cikin ransu suna kuma jiyo taron 'yan suna yadda aketa hira da nishad'i.
ALHAMDULILLAHAnan na kawo k'arshe wannan littafi nawa,kura-kuran danayi cikin rashin sani dama wanda nayishi da sanina Allah ka yafemin👏🏻
Sai kun jini a wani sabon littafin nawa mai fitowa nan bada jimawa ba da yardan Allah mai suna 🦇RAMIN MUGUNTA🦇 karfa ku bari a baku labarin wannan littafi,tabbata yana fitowa a fara karatu dake. Ba zance komai ba bayan wannan😊nagode sosai da soyayyarku Allah yabar zumunci ameen🤝🏻.....
Idan kuna son sabon book nawa naga comment da voting naku
Mmn Shureim

YOU ARE READING
MIEMIE BEE A WANKI GARORI
FantasyLabarine k'irk'irarre na tabbata zai Ilmantar tare da nishad'antar daku,kuci gaba da biyoni karku bari a baku labari... LOVE YOU