[5/8, 8:15 PM] +234 813 737 1414: 💙♥💜💛💚
ZAKISAN KONI WAYE
♥💜💚💛❤
®zuwairat(ummu maryam)7⃣
Har suka kai gida Salem bai bar dariyba,
"Ni ake cewa matsiyaci...gaskiyana tausayawa samari marasa money.. Don gaskiya da gani suna shan wulakanci" daria Abdul dake zaune yayi sannan yace
"Ai sir kadan ne wannan.." Dan tabe baki Salem yayi sannan yace
"Amman wasu yanmata basu da tarbiya..haduwa babu kunya babu tsoro ka zagi mutum"
"Ai sir wasu yanmata har marin samarin suke..." Bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"Kai alh Abdul ..ka bar karya mana...daga inasonka sai mari...ya rabbi kasa incikaro da irin wannan wallahi sai na taya ko waye daukan fansa" shidai Abdul daria kawai yayi don yasan irin wahalan dayasha hannun yanmata kafin ya gama degree dinshi yasami aiki a NGO kuma amatsayin bodyguard din Salem.ONE WEEK LATER
cikin sati daya Salem ya gane abubuwa da dama game da mata don cikin sati dayan kullum sai yaga cool babes amman duk wacce yayiwa maganan so sai su wulakantashi , wasu har da zagi, Amman abun bai bashi haushi don duk sanda mace ta zageshi ko tayi mashi kallon banza sai ya wuni yana daria don dadin abun yakeji cos yanzu zai gane wacce zata soshi don Allah, yasan duk yanmatan dayayi toasting dasun San koshi waye da gudu zasu amsheshi hannu bibbiyu. Kuma yanmatan rashin kula garesu don fuskanshi da kayanshi mara guga kawai suke kallon Amman dazasu kuramashi ido su kalli agogon hannunshi, Rolex watch ne sannan inda zasu kalli zoben azurfan dake hannunshi costumise ne sannan da zasuyi hakuri su kalli kafanshi designer Prada ne kuma inda zasu kalli.hannunshi da kafanshi fari kal suke kaman ka taba jini yafito abunka da bafulatanin cikin daula.
Tunda suka fara fita kullum Salem cikin ciwon kai yake sannan tafin hanninshi yayi ja saboda dan tukin dayake cos rabonda yayi tuki har ya mance sai yanzu.
Duk wacce yadauka sai sun biyashi kudi koda yace baya amsa sai sun tillasa shi ya amsa amman suna bashi yana badawa.
Kuma wannan fitan ya kara wayar mashi da kai don yanzu yasan yakamata masu hali su dinga Dan fita don hakan zaisa su san halin da talakawa suke ciki cos yanzu ya kara sanin da akwai masu wahalan rayuwa sosai. Kullum sai yafita da akalla raw cash na 1million amman bai dawowa dako sisi saboda duk mai baran daya gani sai yabashi rabonshi.
Tunda yake bai taba fita koda abroad yaji it in dadin da yake ji ba cos he's having lots of fun. Haka yasan yayi deciding koda Allah yasa ya samu biyan bukatanshi, duk shekara zai dinga dan fita yana ganin abinda ke faruwa.💛💚💜♥💙💛❤
Ameera ce tsaye cikin wata kayattacen daki, daka gan dakin kasan na yayan hutune, komai na dakin pink sannan ga wata madaidaiciyan plasma jikin bango da decoder, tashar boom TV take kallo don sai wata wakan Stanley enow ke tashi itakuma sai rawanta take, daga ita sai pant da bra sai rasa take kaman ance kiyi rawan zaa baki award. Duk ilahirin jikinta sai shaking yake, bayan wannan wakan aka sawakan sekem aikam nan rawa ya chanza, yanda take rawan tamkar daita akayi rawan sannan kaman itace tayi wakan don babu part din wakan da bata iyaba.
Wayan ta dake kan dan mini bed dinta sai ringing take amman bataji, sai bayan anyi mata 3 miss call sannan daga baya taji da sauri ta rage volume din decoder tare da picking wayan
"Babe ya kike?" Daga daya side din akace
"Haba ameera INA kika ajiye wayanki naketa kiranki ba amsa..." Ameera dake nishi saboda rawan datayi tace
" sorry sis wallahi ina nan INA practicing dance step dina ne...." Bata karasaba yarinyan ta tuntsure da dariya sannan tace
"Practicing kaman dole ko kuma ince kaman za a baki award?"
"Dalla malama what's your reason for calling"
"Daman ummace ta aikeni zoo road shine nace inzo ki rakani?" Ameera kaman jira take
"Yes kizo daman nagaji da gidan nan kuma mom ta hanani fita"
"OK..gani nan zuwa Amman please ki shirya don nasan halinki"
"Don't worry yanzu nan zan shirya" suka katse wayan. Da sauri ameera tabude katon wardrobe dinta Wanda ke shake da kayan sawanta,wash purple Arabian gown ta fiddo tare da Dan figigin Vail din kayan.
Dagudu tashiga bathroom ta watsa ruwa sannan tafito, cikin sauri ta shirya cikin kayan sannan ta dauko makeup kit dinta ta zauna gaban mirronta ta tsara kwalliyanta looking so breathtaking, sannan ta fesa turuka masu kamshin gaske. Wurin shoe rank dinta ta nufa ta dauki wasu light purple high heels sannan ta zauna bakin gadonta tana jiran zuwan kawarta mai suna zeenat.
