Sanadin Gata
By free_boy_
172
9
0
  • Action
  • blog
  • book
  • enjoy
  • free
  • hausa
  • hausafulani
  • hausanovel
  • interesting
  • littafi
  • littafinhausa
  • popular
  • priceless
  • readerxcharacter
  • story
  • trends
  • wattpad
  • wattpaders
  • writer
  • writing

Description

~~Kanta dauke yake da farantin talla wanda aka kasa mata dafaffen rogo da gyada kulli kulli, taci damara sai kace wadda za tayi dambe tana tafe tana rera wakar ta"iye nanaye ayye yaraye nanaye carmama, ina tafiya ta jirgin goro zaya kade ni, jirgin goro kar ka kadeni, jirgin goro zan maka sako, sakon goro ko na turare in kaje kace da uwata, in kaje kace da ubana jirgi yai bari, jirgi yai bari da madaurin aurena, iye nanaye ayye ya raye nanaye carmama, da inna da baba an kawo kudin toshina cacas cas suna kirgawa, sun ganni suna boyewa in kun so kubar boyewa, auren fari sai na zaba sai na zabi wanda na ke so koda soja ko dan sanda, koda kuku koda boyi, koda jinjiri sha mama sai yaci tuwon kwanona sai yasha ruwan kwanona sai na kai ruwa sai nakai ruwa ban daki yai wanka, iye nanaye ayye yaraye nanaye carma....kuluwa, kuluwa kawo rogon, muryar wasu maza masu sai da ruwa ne ya hana kuluwa karasa baitin wakar da take rerawa, cikin sauri ta nufi wurin da suke, tana zuwa ta sauke farantin da ke kanta ta fara kukkulla musu kamar yadda suka saba siya, nan da nan aka warwashe ta dauki farantin ta cikin hanzari bayan ta kirga kudinta ta hada Kansu naira dari biyu cif cif, sauri take sosai dan tasan yanzu iyatu tana nan tana jiran zuwanta.

Part 1

Continue Reading on Wattpad
Sanadin G...
by free_boy_
172
9
0
Wattpad