JARIRI COMPLETE
By AmeeraAdam60
16.2K
1.1K
109
  • Horror
  • gimbiya
  • hausanovels
  • kano
  • littafanhausa
  • love
  • masarauta
  • romance
  • sarauta

Description

A daren ranar da suka koma da daddare kimanin karfe biyun dare Inno ce ta fito fitsari ahanyarta ta dawowa, ta hango ƙaƙanin abu na tafiya idan yayi gaba sai ya dawo baya ya rangwaɗa kai gefe. A ɗan tsoroce Inno ta ce, "Toooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan" ta ƙarasa magana tana haskashi da ƴar fitilarta. A zabure ta ja baya ganin jaririn Nusaiba ne tumɓur ko wando babu, washe mata baki yayi ya dafe ƙeya yana wani irin layi kamar wanda yasha ya maku, cikin wata irin murya ya cafe irin maganar Inno yace, "Tooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan" tana faɗa yana wani irin tsalle kamar zai faɗo kan Inno, wurgar da butar tayi saboda tsoro ta fara gudu. Tsalle yayi ya caɓe zanin Inno har ya taɗe ta ta faɗi da rarrafe ta dingan rarrafawa tana ƙwala ihu, lokacin da ta ƙarasa ɗakinsu tuni ta daɗe da wurgar da zani daga ita sai ɗan fatarinta.

1&2

Continue Reading on Wattpad
JARIRI CO...
by AmeeraAdam60
16.2K
1.1K
109
Wattpad