ANYA BAIWA CE?
By AmeeraAdam60
9.7K
194
29
  • Historical Fiction
  • billynabdul
  • gimbiya
  • kano
  • littafanhausa
  • love
  • nigeria
  • romance
  • sarauta
  • yarima

Description

Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? " Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa. Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba " Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani. Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba."

PAGE 1

Continue Reading on Wattpad
ANYA BAIW...
by AmeeraAdam60
9.7K
194
29
Wattpad