YAWON SALLR HJY IYA...
By AmeeraAdam60
2.6K
467
46
  • Short Story
  • ameeraadam60
  • arewa
  • arewawriters
  • death
  • destiny
  • gimbiya
  • hausanobels
  • iman
  • kano
  • kawaye
  • kuruciya
  • love
  • maraicina
  • marriage
  • masoya
  • mijina
  • nigeria
  • romance
  • soyayya

Description

Gudu yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa. A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar hannuwan sa ya kai musu duka yana fadin, " wallahi bansan da makiya nake tafe ba sai yanxu idan kuka maidani cikin motar nan ban yafe muku ba. Ku sake ni na karasa bichi a kafa, idan kuka kaini mota wallahi alhakin mutuwata a wuyanku yake, cikin hanzari suka kara matsowa zasu kama dan tsoho, aykuwa ya yi sauri ya matsa baya hadi da buga kafa daya, ya kara kwalla kara yana fadin, " yeeeeeeeee ku matsaaaaaaaa ko in ma ke kuuuuuuu, ya karasa fada yana dunkule hannuwa har huci yake. Daya daga cikinsu ya kallin dayen yace, " wai kuwa Anya bazamu kyale tsohon nan ba yaje yayi ta tafiyarsa, tunda anasan ceton rayuwarsa yana san yayiwa mutane illa, kana ganin yanda ya kaimun duka a gefen fuska badan na kauce ba da ya gwabjeni yayi mun mahangurba, " kai haba yanxu tsohon nan ne zai gagaremu, idan aka ce mun kasa kamo shi ba muji kunya ba dan Allah rabu dashi bari kaga muma karfi zamu nuna masa, muna zuwa ciccibarsa zamuyi farat daya zamuyi masa. Aykuwa suka tunkari dan tsoho me buhu, yana ganin sunyo kansa gadan-gadan ya fara kai duka ta ko ina, yana yi yana ja baya sai kuma yayo gaba kamar zai doko wani daga cikin su, yan da kasan yana filin danbe. Basu bi ta kansa ba, sukub haka suka sun kuci dan tsoho suka mammakure hannusa a hammatarsu sai wutsul-wutsul yake da kafafuwa, yanayi yana wani karaji shi bai yarda ba dole kwacewa zaiyi daga hannunsu. Bakin motar suka karaso suna kokarin saka dan tsoho sai fisgewa yake yana ciccijewa har suka samu suka tura shi ciki, wani daga gefe ya dan leko su yana fadin, " to ita ma iya ku sata aciki man, kunga kun huta, idan fa kukayi sake tsohon nan ya kubce wallahi dawa zai shiga, dan na lura motar nan ta tsora tasu dayawa, juyawa sukayi zasu dauko hjy iya.

1&2

Continue Reading on Wattpad
YAWON SAL...
by AmeeraAdam60
2.6K
467
46
Wattpad