KUSKURE DAYA
By Atize21
125
7
1
  • Fanfiction
  • arewa
  • family
  • fate
  • fiction
  • forgiveness
  • hatred
  • hausa
  • islam
  • love
  • peace
  • romance
  • tragedy

Description

Arziqi da yaya sune silar farin ciki a gurin dan adam, a duk inda mutum ya samu daya zai ta qoqari wajen ganin ya samu dayan, in kuwa ya rasa za ka same shi cikin yanayi na rashin walwala sai dai masu tawakkali su kan mi qa ma Allah lamarin su har su kai ga samu abun da suke muradi. A wannan ahalin ba haka bane, haqiqa Allah ya azurta ta su da duk wannan abubuwan har ma da qarin ilmi, wanda shine gishirin zaman rayuwar. amma KUSKURE DAYA ya hana musu samun farin cikin da suke gani gashi daf da su amma ya gagare su samu. **** 'sai yaushe rayuwar mu zata daidaita ne mu ma mu samu daidaito? 'yaushe zamu gane wannan rayuwar mai yanayika mabanbanta inda ta dosa, 'ko yaushe zamu samu farin ciki ---- ko me ta tuna kuma ta gaza qarasa kalmar ta, sai kuma murmushi da ya zo mata a ba zata, tayi shi ba tare da tasan ma murmushin ya subuce mata ba. dan a halin da ta ke ciki wannan murmushin ba gayyatar sa tayi ba,fuskar ta ta dago mai dauke da idanuwanta dara dara masu haske da qyalli gwanin kyau, masu yalwar gashi da kuma cikar gira da ta qara qayata mata su, don in har da ido ake gane kyau to tabbas ita din tana cikin kyawawa, qyallin idanuwan na hango kawae ban samu damar qare mata kallo ba sbd duhun gurin da take zaune, hasken farin wata ne ma ya qara taimaka min gurin gano idanuwan sbd qyallin da sake. 'zaune take ita kadai take ma kanta tambayoyin da bata san amsar su ba, Korda ace wani ta tambaya daga cikin waanda zata iya tambaya amsar dai daya ce, duk a xuci take wannan mahawarar, sai dai tana sane da alqawarin Allah na cewa duk tsanani yana tare da sauqi. inaga wannan dalilin ne ma yasa ta murmusa. **** ku biyoni don jin lbrn wannan ahalin, ahalin malam taju da irin tasu qaddarar a rayuwa, mai dadi da akasin hakan tunda ita rayuwar haka ta gada.

Authors note

Continue Reading on Wattpad
KUSKURE D...
by Atize21
125
7
1
Wattpad