Description
...Shin me yasa mahaifi zai mayar da ƴaƴansa tamkar hannun jarin da zai tsammaci samun riba a ko da yaushe? '''ƊANƊANO..''' •••Hawaye sosai suke saukowa idonta da wani irin Baby voice tace "ban yi sallama da su Yaa Aalima ba" Hamdiyya dake kusa da ita ta kalleta tace "ohh! Bari a kirasu sai kuyi sallama a gurguje kinga yanzu muna sauri ne kada dare yai mana,hanyar Abuja babu kyau kwanakin nan" ita dai bata sake cewa komai ba kuka kawai take kamar ranta zai fita,Hamdiyya ta sauke glasses ɗin gefenta ta kalli Baffa dake tsaye tace "Baba tana son yin sallama da su Aalima wai" Baffa ya kalleta ji yake kamar zai daketa,ya daure yace "ahh tou! Ta jira bari su fito suyi sallamar daga nan" da wani irin sauri yana kaɗa babbar rigarsa ya koma cikin gidan ya kira ƴan uwanta da sukayi cirko² a tsakar gidan tunda suka ga fitarsu,yana shiga gidan ya kallesu yace "kuzo kuyi sallama da su" da sauri duk suka biyoshi su uku,Aalima tana kuka tun bata ji abunda yake faruwa ba,amma ganin yanda Baffa ya ɗauki kayan ƴar uwar tasu ya tabbatar mata da wani wajen za'a tafi da ita,ta kusa da gefen Hamdiyya duk suka tsaya,a hankali ta ɗago tana kallon su da tashin hankali tace "Yaa Adija dan Allah kice da Baffanmu ya barni a gurinku,ni ba na son binsu,na yarda yai min auren da yace,amma dan Allah kada ya rabani da ku,pleaseee" babbar cikinsu da ta kira Adija ta juya ta kalli Baffa hawaye suna cika mata idanu tace "Baffa ina za'a tafi da ita?" Yace "aiki za ta je idan ta gama za ta dawo" Adija tace "yaushe? Wane irin aiki ne Baffa? Me yasa sai *FANNAH* Baffa? Madadin ka turani ko Ashey,ko Aalima.." Ƙalubale gareku iyaye masu son yin kuɗi ta kowane hanya...