AL-MAJIRA Complete
By Jeeddahtou
4.0K
70
1
  • Short Story
  • haske
  • writers

Description

*T*afiya take cikin nutsuwa, amma kallo d'aya xaka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin matsananciyar damuwa" yarinya ce 'yar kimanin shekara sha biyar d'auke da buhun bacco a hannunta, tafiya kawai take ba tare da tasan ina ta dosa ba. bakin wata bishiyar darbejiya ta samu ta d'an tsaya domin ta samu hutu ko xuciyarta ta sarara daga tafasar da take yi mata. a hankali ta saukar da ajiyar xuciya sa'annan tayi duba i xuwa jakar da kayanta ke ciki. nan da nan idanuwata suka cika fal da hawaye, ta fad'a a ranta *ALLAH KA FINI SANIN HALIN DA NAKE CIKI* kuka mai tsanani ta cigaba da yi kanta na sunkuye a jikin jakarta, da taga ba sarki sai Allah kukan ba xai kaita ba, sai ta yanke shawarar cigaba da tafiya, duk da dai ba ta ji a ranta xata iya cigaba da tafiyar, saboda yunwa da kishiruwar da suka addabeta. a hankali ta cigaba da jan 'kafa cikin 'karfin hali har ta isa i xuwa wajen da mutane suke, ta samu gefen wajen ta ajiye jakar da 'yan *tsummokaranta* suke ciki. ta 'karasa wajen da wata mai abinci take, da xuwanta sai taga idanun mutane duk sun dawo kanta, cikin hanxari mutanen suka tashi a guje, ciki kuwa har da mai abincin, ashe bisa tsammaninsu suna zaton *MAHAUKACIYA CE* d'aya daga cikinsu ne kawai ya yi 'karfin hali ya'ki guduwa, cikin zafin rai yake tambayarta "ke me kike bukata a nan"??? cikin rawar murya ta amsa masa da cewa "ni *AL-MAJIRAH* ce sadakar abinci ko kudi nake son ku taimaka min dashi tun safe babu abinda nasa a bakina. tsawa ya daka mata wanda yasa har sai da ta firgita "ina ruwanmu da almajirancinki nauyin ciyar da ke a kanmu yake, mu muka sa iyayenki su kawoki bara su wulakanta baiwar da Allah ya basu?? kauce min da gani kafin na doka ball da ke" bata san lokacin da hawaye masu xafi suka rufe idonta ba har ya xamto bata iya ganin hanya, jiri taji ya d'ebeta kamar xata fad'i, Allah dai ya kiyayeta bata fad'i ba. lallai wasu mutanen ba su da tausayi, ta fad'i hakan a ranta.

ALMAJIRA Babi na daya

Continue Reading on Wattpad
AL-MAJIRA...
by Jeeddahtou
4.0K
70
1
Wattpad