Description
Season 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sallamar Almajirin ne ya katse masu hanzari wajen ci gaba da yin firarsu, a gurguje Aunty Rukayya ta tashi ta anso kwandon ta karasa da shi ciki, inda tana aje kwandon ta nufe kitchen ta dauko flat-flat amma kafin ta kai ga shiga kitchen ta soma tambayar Hajiya kaka da ce wa "farfesun kadai kike son a zuba maki, ko harda shinkafa? dan ina da tabbacin ce wa wannan karon tun da muka ga kula biyu, jaluf-rice ce aka mana!" Hajiya kaka ta ce "Ni dai na fi son farfeson nan, dan ba wata yunwa ce nake ji ba." Aunty'Rukayya ta ce "To shikenan Hajiya" tana mai kara kurdewa cikin kitchen din, cikin d'aukar wata wak'a ta Umar M Shareef abakinta cikin d'ora kalmominta a kai, inda kuma tana fitowa daga cikin kitchen, ta kara daga sautin muryar yanda wakar zata fi dadin saurare, ta ce "Ai wannan abinci ya haɗu, ɗinɗirin-ɗiri ɗinɗin, wannan dai abinci ya haɗu, ɗinɗirin-ɗiri ɗinɗin, Sai fa ƙamshi yake famar fita, ɗin ɗirin-ɗiri ɗinɗin........" Inda direct kular Farfesu ta buda dan ganin farfesun abinda aka yo masu, wanda har ta fara saka ranta da kaza. Sai dai kuma wani abin ban mamaki tana bude kular farfesun a maimakon taga kazar! sai taci karo da kawunan kifafe guda hudu, sai tulin kabewa da aka sassarata manya-manya aka saka kamar wani k'aton yanka na nama...