TAFARU TA K'AR...
By 68Billygaladanchi
172.6K
15.1K
1.1K
  • Random
  • jolinsky
  • mrs

Description

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunanin ka, na Amince zan rayu dakai rayuwa ta amana daso dakuma k'auna" ka tallafi rayuwata kadena fad'ar hakan kaji" Cikin azabar ta ciwon dayake ciki ya saki wani murmushi dayake nuna tsantsan jin dad'in da kalaman ta suka saka shi ya ce..."Naso ace kin furta mun wannan kalman tuni amma ko yanzu naji dad'i sosai, dad'in dana tabbatar dashi zan mutu a raina, My meenal zo matso kusa dani kinji?" da sauri ta k'arisa kusa dashi da rik'o hannun shi tace "kaga yanda kake numfashi ko yaa muhammad? ka daure ka dena magana kafin likitan yazo, save ur strenght plss" K'walla ya gangaro masa da k'yar ya iya furta "Wanda yake bayarda ikon numfashin ya buk'aci abinsa my meenal, lokacin tafiyane yazo tafiyan daba fashi, dukkanin abinda ya faru tsakanina dake na yafe miki matsayina na mijinki ina mikin fatan aljannar firdaus mad'auka kiya, ki sani inajin tsoro wlhy, tsoro nakeji my meenal" kuka ya k'wace mata sosai ta sanya kukan kuwa "Mesa kakemun maganganu a baud'e, wlhy ina fahimtar komai yanzu, hausarka tangaran nake fahimta mutuwa kake nufi zakayi bana fata kuma, kayi shiru kaji" Hannunsa d'aya ya mik'o mata wani takarda ta karb'a ya k'ara had'e hannun shi da nata da takardan, yace yana numfarfashi da k'yar "Ki bi abinda na rubuta a takardan nan, ki karantashi cikin nutsuwa kinji" batace komai ba daga ita har k'aninsa dake nan kusa da ita se gani sukayi yayi shiru bakinsa yana motsi amma basajin meyake cewa numfarfashi kurun yake sama sama, daganan sekuma yae shiru komai ya tsaya cak rai yayi halinsa!!!!!!!

Untitled Story Part

Continue Reading on Wattpad
TAFARU TA...
by 68Billygaladanchi
172.6K
15.1K
1.1K
Wattpad