auren fari
By ItzmeMustapha
1.8K
72
16
  • Adventure

Description

AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣4⃣ *DAFATAN ZAKU SAKA TA ADDU'A AKODA YAUSHE HAJIYA RABI BADAWI MAMAN IBRAHIM DA NURY* .............. *Ke tsaya* ya daka ma umaimah tsawa, ya isa gun mamee da sauri , kiyi hakuri mana. Na ce kamun laifi ne? Tunda ka rainani to bazata kara rabarka ba har ka gana mata azaba......wace azaba mamee ya marairaice, gyaran da zatayi mun shine azaba? Ta kalli umaimah *Na ce ki shiga ciki ko?* Ya mike tsaye *ke kina hauka ne?* ya kara daka mata tsawa ......wai mamee menene haka? Ya kalli umaimah dake niyyar shigewa ya ce *wallahi kika shiga zan fiddo ki* .......wai mamee menene haka? Duk ya rikice, ya kalli umaimah dake makale a bango *Malama kiyi mata bayani* ...ya juya mamee wallahi bazan mata komai ba gata nan tambayar ta. Kinyi shiru mamee....me zance tunda ka rainani ka nuna ban isa ba? Duk lokacin da ta hau saman da kuka take saukowa ka zageta tsaf ka gama.......Qalu innalillahi mamee ki sassautan mana. Ya maka wa umaimah harara *Wai bazakiyi magana ba?* Ta ce me? Mamee na tuba dakin can yayi kura....... Shin naji na amince gyara kake so? Zauna ga kujera *Uwani je ki gyaro ki dawo* Simi simi zata wuce ya mike *Ta koma kawai bana so*......fuuu yayi sama. Uwani jeki ciki abinki kinji ko? Tana juyawa wayar ta tayi kara tayi ciki da hanzari. Hello *Sato ki taho don Allah* Tabb wallahi mamee na falo.......ke da waye a waya? Tayi saurin latsewa......ni... Nida luba ta juya tana kakkabe gado. Ya zaro ido *Wayar ma hanawa zatayi?*

24

Continue Reading on Wattpad
auren fari
by ItzmeMustapha
1.8K
72
16
Wattpad