MAKANTAR ZUCI
By Ummu-abdoul
19.2K
2.9K
1.0K
  • Mystery / Thriller
  • death
  • fikrawriters
  • hausa
  • rebuildhumanity
  • sccvolunteers2017
  • truestory
  • ummuabdoulwrites
  • witchcraft

Description

Rayuwa kan zo ma kowa da kalar qaddarar sa, walau khairan ko akasin hakan. A duk yanda ta zo maka da kamata yayi ka rungume shi cikin gode ma Allah akan sauran ni'imomin da ya maka ba tare da sanya damuwa ba. Zainab (Amra) da Fatima (Amma) suna cikin ya'yan da duk faɗin unguwar su babu kamar su. Ba unguwar kaɗai ba hatta dangin su ba wanda ya samu gata sama da su. Mahaifin su ya yi kokarin saka su a makarantu masu tsada don yana biyan sama da miliyan a kudin makarantar kowacce a cikin su, sannan daidai da ruwan da su ke sha ya tabbatar da mai tsada ce. Hakan ya sa mutane ke jin haushin mahaifiyarsu da duk da faɗin ya maida aurensa da Mahaifin su yayi a kanta, kin dawowa ta yi. Mutane kan kira ta da sakarya mai gudun arziki, wasu na dangantata da wa'inda ko a duniya ba su da rabo balle a kiyama, duk ta haɗa tayi biris da su har sai lokacin da amaryar sa ta kama shi dumu-dumu yana aika aika da ɗiyar cikin sa. "Anty duk ranar da kika san wani irin miji kike aure zaki dena biye masa wajen tsine min, sannan za ki yi da na sanin kasantowarshi cikin qaddarar rayuwar ki" su ne kalaman da ya dawo mata sabuwa a zuciya, rufe ido tayi cikin burin ta bude su akan Amma ko ta nemi gafaranta amma inaa Amma tayi mata nisa, nisan da ba zata iya kamo ta ba balle har ta nemi gafaranta. BAN YARDA A KWAFE MIN SHI DAGA KAFAR WATTPAD BA, YIN HAKA SHIGA HAKKI NE. ZAI DINGA ZUWA SAU ƊAYA A SATI SANNAN RANAR DA AKA KAMMALA ANA IYA NEMAN SA A RASA SAI A SHAFIN OKADA. INA SONKU IRIN SOSAI DA SOSAI DINNAN. INSHA'ALLAH BA ZA KI YI DANA SANIN TAFIYAN NAN BA.

Marhabin

Continue Reading on Wattpad
MAKANTAR...
by Ummu-abdoul
19.2K
2.9K
1.0K
Wattpad