REAL-SMASHER's Reading List
10 stories
IFZAA! (MMBFF) by REAL-SMASHER
IFZAA! (MMBFF)
REAL-SMASHER
  • Reads 27,349
  • Votes 2,219
  • Parts 34
(MARRIED TO MY BEST FRIEND FATHER) ...A hankali na nisa na ƙarasa kusa da ita na zauna,ina kallon frame ɗinmu dake ajiye saman bedside drawer nace "wai me kika ɗauki kanki?" Tace "yanda kika ɗauki kanki nima haka ne" da sauri na juya na kalleta,lokaci ɗaya na ɗauke kaina ina taɓe baki nace "ni yanzu idan na amsa nace miki zan iya kallon Daddy matsayin miji wallahi na yi miki ƙarya" tace "ko saboda me?" Nace "saboda shi ya raine ni,can't u think me mutane za suce idan haka ya faru? Cewa fa za ayi.." Widad tace "kin auri mahaifin ƙawarki?" Da sauri na gyaɗa mata kaina nace "sure! Kuma ko bayan haka ai kin ga abun bai tsari ba,tunda shi ya raine ni tun ina yarinya,dan Allah kawai sai na auresa kuma? Shi fa Daddy ne" murmushi Widad tayi tace "tou dan shi Daddy ne sai me? Ai dai naga babu haramci dan kin auresa" cikin sauri nace "ehh! Na san ba haramci amma.." Widad tayi saurin katse ni tace "tou tunda kin san haka why baza ki amince ba,kinga duk abunda mutane za su faɗa sai suyi with evidence,kin san dai shi mutum ba'a iya masa" nace "ni fa Widad kin kasa fahimta ta" tace "kuma wallahi bazan fahimce ki ba,muddin baki yarda da abunda nazo da shi ba.." Ƙaƙa-ƙara ƙaƙa! Kou yaya za'ayi wannan rayuwar auren tsakanin ƴar riƙo da mahaifin ƙawarta? Shin za ta amince ne ko a'a? To find out how the story will turned out,just follow this fairy tale of love and romance.
ALK'AWARIN JINI (BLOOD PLEDGED) COMPLETED.✔ by REAL-SMASHER
ALK'AWARIN JINI (BLOOD PLEDGED) COMPLETED.✔
REAL-SMASHER
  • Reads 39,495
  • Votes 2,771
  • Parts 62
#Love & Destiny.
DAUƊAR GORA! by REAL-SMASHER
DAUƊAR GORA!
REAL-SMASHER
  • Reads 5,548
  • Votes 377
  • Parts 22
...Labarin ƙaddarar AYSHATOU AYATULLAH wacce tayi fama da matsalar yoyon fitsari at a very young age,she really went through tsananin rayuwa,kowa yana ƙyamar zama da ita,saboda larurar da ba ita ta sawa kanta ba,shin za ta warke ne kou a'a,me zai faru da rayuwarta a gaba?
KALLO YA KOMA SAMA! by REAL-SMASHER
KALLO YA KOMA SAMA!
REAL-SMASHER
  • Reads 2,411
  • Votes 191
  • Parts 11
... KALLO YA KOMA SAMA! Hausawa suka ce SHAHO YA ƊAUKO GIWA. Anya kuwa haka yana iya faruwa,duk girman GIWA ace SHAHO ya ɗauke ta? Duk lalacewar GIWA ko ta mutu ta fi ƙarfin jan KIYASHI..
MANAR by REAL-SMASHER
MANAR
REAL-SMASHER
  • Reads 4,372
  • Votes 378
  • Parts 14
The way we were before...
WAZEER! by REAL-SMASHER
WAZEER!
REAL-SMASHER
  • Reads 5,033
  • Votes 359
  • Parts 32
...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ɗansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this fairy tale of love,jealousy and ultimate betrayal that leads someone to the lost end..
WANI AL'AMARIN.! COMPLETED✔ (WARWARESHI SAI ALLAH) by REAL-SMASHER
WANI AL'AMARIN.! COMPLETED✔ (WARWARESHI SAI ALLAH)
REAL-SMASHER
  • Reads 75,181
  • Votes 5,162
  • Parts 80
#Royalty & Revenge
IN-LAWS by REAL-SMASHER
IN-LAWS
REAL-SMASHER
  • Reads 1,501
  • Votes 148
  • Parts 7
...He was married to her elder sister,sannan ita kuma yana sonta,even though ya san ƙaddara ta haramta masa ita matsayin mata matsawar yana tare da ƴar uwarta,hakan bai sa ya haƙura ya cire son da yake mata a ransa ba,shin ya ya al'amarin zai tafi? Sakin ƴar uwarta zai ya aureta? Ko kuwa zai jira faruwar wani al'amari daga Ubangiji da zai halatta masa aurenta ne?
CIWO A JIKIN WANI! by REAL-SMASHER
CIWO A JIKIN WANI!
REAL-SMASHER
  • Reads 1,095
  • Votes 87
  • Parts 11
...Shin me yasa mahaifi zai mayar da ƴaƴansa tamkar hannun jarin da zai tsammaci samun riba a ko da yaushe? '''ƊANƊANO..''' •••Hawaye sosai suke saukowa idonta da wani irin Baby voice tace "ban yi sallama da su Yaa Aalima ba" Hamdiyya dake kusa da ita ta kalleta tace "ohh! Bari a kirasu sai kuyi sallama a gurguje kinga yanzu muna sauri ne kada dare yai mana,hanyar Abuja babu kyau kwanakin nan" ita dai bata sake cewa komai ba kuka kawai take kamar ranta zai fita,Hamdiyya ta sauke glasses ɗin gefenta ta kalli Baffa dake tsaye tace "Baba tana son yin sallama da su Aalima wai" Baffa ya kalleta ji yake kamar zai daketa,ya daure yace "ahh tou! Ta jira bari su fito suyi sallamar daga nan" da wani irin sauri yana kaɗa babbar rigarsa ya koma cikin gidan ya kira ƴan uwanta da sukayi cirko² a tsakar gidan tunda suka ga fitarsu,yana shiga gidan ya kallesu yace "kuzo kuyi sallama da su" da sauri duk suka biyoshi su uku,Aalima tana kuka tun bata ji abunda yake faruwa ba,amma ganin yanda Baffa ya ɗauki kayan ƴar uwar tasu ya tabbatar mata da wani wajen za'a tafi da ita,ta kusa da gefen Hamdiyya duk suka tsaya,a hankali ta ɗago tana kallon su da tashin hankali tace "Yaa Adija dan Allah kice da Baffanmu ya barni a gurinku,ni ba na son binsu,na yarda yai min auren da yace,amma dan Allah kada ya rabani da ku,pleaseee" babbar cikinsu da ta kira Adija ta juya ta kalli Baffa hawaye suna cika mata idanu tace "Baffa ina za'a tafi da ita?" Yace "aiki za ta je idan ta gama za ta dawo" Adija tace "yaushe? Wane irin aiki ne Baffa? Me yasa sai *FANNAH* Baffa? Madadin ka turani ko Ashey,ko Aalima.." Ƙalubale gareku iyaye masu son yin kuɗi ta kowane hanya...
MAKTOUB by REAL-SMASHER
MAKTOUB
REAL-SMASHER
  • Reads 3,442
  • Votes 341
  • Parts 16
Nowadays,the words "betrayal" and "deception" is more effective than anything else in the life of humanity... Ya ya za kiji a lokacin da kika bud'a ido kika tarar mutanen da kika amincewa fiye da kowa,kika d'auke su kika kaisu wani matsayi,har kike gani da jin duk duniya ba ki da kamarsu.. Sai a dai² lokacin da ba ki tsammani ba,baki tab'a tunanin cewa wannan mutanen za su iya cutar da rayuwarki ba,suka shirya miki yaudara,suka ci amanar ki,bayan kin yi hak'uri,kin manta da duk wani alak'ar da ya tab'a had'a ki da su a tarihin rayuwarki.. Rana d'aya,lokaci d'aya sai suka dawo gare ki,shin wad'annan mutanen sun cancanci ki yi musu afuwa ko kuwa za ki d'auki FANSAR abunda suka aikata miki? To find out... #Just follow this twisted tale of love,deception,jealousy and ultimate betrayal that leads to an intense love triangle in the lives of:Aadil,Fawad,Barraq,Ismat and Badriyah...